Labaran Duniya

Ban yi murnar rasuwar Abba Kyari ba – Kwamishinan da Ganduje

Ban yi murnar rasuwar Abba Kyari ba – Kwamishinan da Ganduje

Gwamnatin Kano ta ce kwamishinan ya ci mutuncin ofishinsa
Kwamishinan ayyuka Injiniya Mu’azu Magaji da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tube ya nemi gafara kan abin da kalamansa suka janyo kan rasuwar marigayi Abba Kyari shugaban ma’aikata a fadar shugaban Najeriya.

A ranar Asabar ne gwamnan Ganguje ya tube Engr. Mu’azu Magaji daga kujerar kwamishinan ayyuka bayan wallafa bayanai a Facebook da suka nuna yana murnar rasuwar Abba Kyari wanda Allah ya yi wa rasuwa ranar juma’a da dare.

Injiniya Muazu ya wallafa a Facebook cewa, “nasara, nasara. Najeriya ta tsira, Abba Kyari ya mutu a cikin annoba..

Wadannan kalamai sun janyo masa kakkausan suka daga mabiyansa a shafin Facebook, inda wasu suke cewa bai kamata mai mukami kamar sa ya yi kalamai irin wadannan ba.

Nan take kuma gwamna Ganduje ya tube shi daga mukaminsa na kwamishina.

Sai dai kwamishinan wanda bai musanta cewa ba shi ya wallafa bayanan ba, ya yi nadama a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce rashin fahimtar bayanan da ya wallafa a Facebook aka yi, har ta kai ga daukar matakin tube shi daga mukaminsa na kwamishina.

“Ina neman gafara ga duk wani abin da ya haifar da rudani, da martani, dukkaninmu muna cikin mawuyacin lokaci na damuwa inda damuwa da kunci ke sa da wahala a iya bambance fahimta da rashin fahimta.”

“Na yi nadama kan duk wani bakin ciki da na janyo wa iyalan marigayi shugaban ma’aikata a fadar shugaban kasa da kuma maigida na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

“A matsayina na musulmi kuma dan Najeriya, mutane ba su fahimce ni ba, har suka yi tunanin wai na yi murnar rasuwar Abba Kyari, inda a gaskiya ban yi ba.”

“Na tura sakwannin jimamin rasuwar Kyari a shafina na Facebook, ta hanyar mai taimaka min na musamman amma mutane ba su ce komi ba amma sai suka fi mayar da hankali kan bayanin da na wallafa suka bada wata ma’ana ta daban don bata min suna a matsayi na mamba a gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje kuma mai biyayya da jam’iyyar APC,” in ji shi.

Ya kuma ce: “amfani da Kalmar nasara nasara, wani yunkuri ne don bayyana alkawalin musulunci kan mutanen da suka rasu sanadiyar annoba. Marigayi Abba Kyari ya rasu sakamakon cutar Covid 19, wanda ya sanya shi cikin wadanda suka yi shahada.”

“Mutuwar Mallam Abba Kyari babbar nasara ce gare shi, wanda shi ne burin kowane musulmi.”

Sai dai kuma game da bayanin ofishin mamacin da tsohon kwamishin ya yi, ya ce shawara ya ba shugaban kasa Muhammadu Buhari.

“Dama ce ga Najeriya ta sake fasalta ofishin shugaban ma’aikatan, inda na yi kira ga shugaba Buhari ya tabbatar da amfani da kalubalen annobar ta hanyar rage karfin ofishin domin tabbatar da ci gaban ayyukan gwamnati cikin gaggawa wanda shi ne fiye da komi da mulkin demokuradiyyar da ke son cimma.”

Kan batun tube shi da aka yi ya ce wasu ne suka sauya ma’anar abin da ya wallafa a Facebook wanda ya janyo ya rasa kujerarsa.

Ya ce, “A matsayi na musulmi ba zan taba yin murnar mutuwar wani dan Adam ba, domin ya saba wa al’adata da kuma koyarwar addinina

Daga karshe Injiniya Mu’azu ya yi wa marigayi Abba kyari addu’ar Allah Ya ba shi Aljannah Firdaus ya kuma ba iyalinsa hakurin rashi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button