Abin Alajabi

Ban Sani Ba Ko Mijina Yana Raye Ko Ya Rasu Tun Bayan Kamashi Da Jami’an Tsaro Suka Yi Kusan Shekara Biyu, Cewar Hussaina Yunus

Ban Sani Ba Ko Mijina Yana Raye Ko Ya Rasu Tun Bayan Kamashi Da Jami’an Tsaro Suka Yi Kusan Shekara Biyu, Cewar Hussaina Yunus

Hussaina Yunus mazauniyar garin Kano ce kuma matar wani dan kasuwa da jami’an tsaro suka tafi da shi fiye da shekara daya kenan babu labarin sa.

A hira da tayi da manema labarai a garin Abuja, Hussaina ta yi kira ga gwamnatin Buhari da ta waiwaye ta da idon rahama a sako mijin ta da ke tsare sannan bata san inda yake ba.

“Kamar yadda maigida na ya sanar da ni bayan ya dawo daga wajen aiki da yamma wata rana kafin a tafi dashi. Muna zaune haka sai aka kira shi aka ce masa wai jami’an tsaro sun kama wani abokin sana’ar sa mai suna Mal. Lawal a hanyan su ta zuwa gida, wai ana masa zargin dan Boko Haram ne.

“Daga nan sai maigida na ya fara cewa ya gode wa Allah da asirin wannan abokin nasa ya tonu yana mai cewa a she shi ya san ko shi waye ya zauna tare da su, da ya ja musu bala’i.

“Ana nan ne fa sai kuma maigida na mai suna Ahmed Mohammed yake sanar da ni cewa wai sun hada kudi da shi Mal. Lawal din sun siya mota domin su siyar su sami riba domin sana’ar sa kenan.

“Bayan kwana uku sai Sarkin kasuwa a nan Kano ya kira shi ya ce masa wai ya nemo kudin da suka siya motar nan tare da Mal. Lawal. Sai ya tafi ya gaya wa mahaifin sa. Daga nan sai mahaifin na sa yace kada ya ba ‘yan uwan Mal. Lawal kudin yaba hukumar Kasuwa.

“Daga nan sai aka siyar da mota aka ware wa Mal. Lawal kason sa. Bayan wata shida, wata rana ya tafi wajen aiki sai ya kirani ya sanar dani cewa jami’an tsaro sun taho kasuwar sun tafi da wani Alhaji Garba da tare suka hada kudi suka siya motar.

“Haka nan ne fa kawai sai bamu kara ji daga gare shi ba. Aka gaya mana cewa jami’an tsaro sun tafi da shi cewa suna binciken ko da gaske ne yana da alaka da wannan Mal. Lawal din da suka yi harkar mota da.

“Yanzu shekara daya da wata 5 kenan bamu ji daga gare shi ba kuma ma ba mu san inda yake ba yanzu.” Inji Hussaina

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button