Labaran Duniya

Bakin talauci ya kai wasu ma’aurata ga sayar da sabon jaririnsu akan N250,000

Rundunar Yansanda ta musamman dake karkashin ikon babban sufetan yansandan Najeriya ta samu nasarar damke wasu ma’aurata da suka sayar da jaririnsu mai kwana daya a duniya akan kudi naira dubu dari biyu da hamsin a karamar hukumar Oyigbo na jahar Ribas. 

Majiyar mu ta ruwaito ma’auratan, Richard da Chidinma sun bayyana ma Yansanda cewa sun yanke shawarar sayar da dan nasu ne domin su samu saukin bakar talaucin da suke fama da shi a rayuwarsu, tare da tashi daga kauyensu don samun ingantaccen rayuwa a birni. 

A ranar 7 ga watan Oktoba ne Chidinma ta haifi jaririn nata a wani asibiti mai zaman kansa, sa’annan ta sayar da shi ga wata mata mai suna Rose Onyia akan kudi N250,000, inda ita kuma Rose ta sayar da jaririn ga wata mata dake safarar mutane, Eucharia Jaja akan kudi naira dubu dari biyar da hamsin (N550,000), wanda ta sake sayar da jaririn da wasu mutane a Legas. 

“Mun sayar da jaririnmu ne ga wata mata mai suna Rose, yara na hudu, kuma daya ya mutu, kwanansa daya a duniya muka sayar da jaririn akan kudi N250,000, amma da izinin mijina na sayar da shi. 

So muke mu tashi daga kauyenmu saboda muna cikin bakar talauci. “Mijina baro yake turawa, don haka muna ganin idan har muka sayar da jaririn zamu samu isashshen kudin da zai kai mu garin Umuahia ko Fatakwal don mu fara sabon rayuwa acan.” Inji mahaifiyar jaririn. 

Shima mijinta, Benson Richard ya tabbatar da talaucin dake damunsu, inda yace saura kiris talauci ya kashesu, kuma matarsa na da katon gyambo a kafarta wanda har ya kan hanata tafiya, don haka suna bukatar kudin kulawa da ita. 


A nasa jawabin, mataimakin kwamishinan Yansandan jahar, Bennneth Igwe ya bayyana cewa sun kama mutane goma sha uku dake safarar mutane, ciki har da ma’auratan a kananan hukumomin Oyigo da Ikewerre na jahar Ribas. 

“Rundunar IGP sun kai samame a Otal din Afrique dake unguwar Afam, cikin karamar hukumar Oyigo dake jahar Ribas, inda muka suka ceto mata shida masu dauke da juna biyu, ana amfani da Otal dinne wajen safarar kananan yara.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button