Labarai

Badakalar Ganduje: Shugaba Buhari ya ce zasu dau mataki akan Ganduje da zarar lokaci yayi

Daga jaridar daily nigerian 

Daga kasar Faransa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar zasu dau mataki akan Gwamna Ganduje daga zarar jami’an tsaro sun aiko da rahoton kan bidiyon da aka ga Gwamna Ganduje na zura dalar Amirka a cikin babbar tiga.
Lamarin ya faru ne a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari yake amsa tambayoyi daga ‘Yan Najeriya mazauna kasar ta Faransa. Tun da farko wani dalibi ne yayi kira ya Gwamnatin Shugaba Buhari akan tayi koyi da Gwamnatin Ganduje wajen bayar da talkative karatu.
Inda nan take Shugaba Buhari ya baiwa dalibin amsa da cewar yaga bidiyon da aka nuno Ganduje yana zuba dalar Amirka a cikin babbar tiga?
Shugaban ya Kara da cewar jami’an tsaro suna duba bidiyon da zarar kuma sun kammala bincikensu, Gwamnatin zata dau mataki kan Gwamna matukar an tabbatar ya aikata laifin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button