Labaran siyasa

Badakalar $5m: Yau Juma’a Ganduje zai bayyana gaban majalisar dokoki ta Kano

Zargin cin hancin $5m: Yau Juma’a Ganduje zai bayyana gaban majalisar dokoki ta Kano

A yayin da zargin da akewa gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ke ci gaba da daukar zafi, musamman bayan bayyanar wani sabon bidiyo, wanda aka nuna Gwamnan sanyen sa bakaken kaya, yana karbar wasu kullinnkudaden; a yau ake sa ran Ganduje zai bayyana gaban kwamitin mutane 7 da majalisar dokokin jihar ta kafa don bincike kan wannan zargi.

A cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan wata, 31 ga watan Oktoba, 2018, wacce ofishin gwamnan jihar ya samu kuma ya buga mata hatimin karba daga majalisar dokoki ta jihar, takardar dai ta sammaci ce, inda kwamitin majalisar ya bukaci Ganduje da ya bayyana gabanta a yau Juma’a, 02 ga watan Nuwamba, 2018 don amsa tambayoyi kan zargin da ake masa.

Daga cikin abubuwan da kwamitin ya bukata, akwai bukatar wasika mai dauke da kwanan wata da hatimin gwamnan, kafin zuwan ranar da zai gurfana gaban kwamitin. Banda wannnan, kwamitinn ya baiwa gwamnan damar zuwa gabanta da lauyansa idan har ya bukaci hakan.

Rahotanni sun bayyana cewa kwamitin da ke bincike kan zargin, sun aikawa gwamnan da wasikar dauke da faya fayin bidiyon da aka hasko shi yana karbar kudaden cin hancin, kamar dai yadda mawallafin jaridar Daily Nigeria, Jaafar Jaafar, ya gabatar masu a makon da ya gabata.

Wata majiya daga majalisar dokoki ta jihar ta tabbatar da cewa gwamnan jihar zai gurfana gaban kwamitin da misalin karfe 10 na safiyar yau Juma’a.

Idan za a iya tunawa, a makon da ya gabata ne wallafin jaridar Daily Nigeria, Jaafar Jaafar ya bayyana gaban kwamitin don amsa tambayoyi kamar yadda kwamitin ya aike masa da takardar bukatar hakan.

Source: hausa.legit.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button