Labaran siyasa

Babu abinda na sani game da bidiyon ganduje-kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kum dan majalisar dattawa mai wakiltan Kno ta tsakiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karyata rahotannin da ke jinginashi da bidiyon karban cin hancin da ake zargin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da su. 

Yayinda yake mayar da martani ga kwamishanan yada labaran jihar Kano, Malam Muhmmad Garba, inda yace mawallafin jaridar Daily Nigerian, Ja’afar Ja’afar na aiki da yan adawa ne kuma makiyin jam’iyyar All Progressive Congress, APC ne, Kwankwaso ya ce bai da wata alaka da dan jaridan.

Ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa, Hajiya Binta Sipikin. Tace: “Kowa dai ya san Jafar Jafar dan jarida ne mai zaman kansa. Kana kamfanin jaridarsa, Daily Nigerian, jarida ce mai zaman kanta” “Babu wata alaka ko cinikayya tsakanin Jafar da Dr Rabiu Kwankwaso. Saboda haka idan suna zargin wani abu, su kawo hujja.” Mun kawo muku rahoton cewa Sanata Barau Jibril wanda ke wakiltar Arewacin Kano a Majalisar Dattawa yayi Allah-wadai da bidiyoyin da ya kira na kage da aka fitar inda aka ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yana karbar cin hancin Daloli. Barau Jibril ya bayyana cewa an yi wannan danyen aiki ne domin kurum a batawa Gwamnan wanda yake bakin kokarin sa suna a idon jama’a. Sanatan ya kara da cewa an yi amfani da fasahan zamani ne wajen ci wa Gwamna mutunci. 


Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button