Raayi

BA ZINA BACE KAWAI BASHI INJI FATIMA MUHAMMAD

BA ZINA BACE KAWAI BASHI INJI FATIMA MUHAMMD

Ita kanta yaudarar “Ya’ya Mata da bata musu tarbiyya WALLAHI itama bashice Kuma idan kaci Sai ka biya

“Ya’ya Mata a duk inda suke amana ce agaremu Koda daga Kai Sai itane to Allah ne cikon na ukun ku.

Mahaifiyarka macece.
Kanwarka macece.
Yayarka macece.
“Yar cikinka macece.
Kakarka macece.

Shin kana tunanin Allah zai barka idan kayi sanadin bata rayuwar Kanwa ko “Yar wani
Babu shakka Bariki da kuma iskanci suna da Dadin gaske musamman awurin fasiqin Dan Bariki.
Yadda ka bata rayuwar “yar wani wallahi kaima komai tsawon Zamani Kuma komai addu,arka Sai wani ya bata taka.
Hatta wasannin banza tsakanin mace da namiji ko Kuma yaudara tareda hure musu kunne, duk suma bashine Kuma wallahi Sai ka biya
Mata suna da rauni mu tausayawa rayuwarsu.
Kada kayi amfani da talauci ko rashin da wata ke ciki kabata Kudi ka keta Mata alfarma wallahi kaima Sai wani ya keta Alfarmarka, wallahi Sai ka zubarda hawaye da idanunka Wata Rana
Mu girmama Mata.
Mata iyayenmu ne.
Mata ababen girmamawane.
Ubangiji ka tsare Imaninmu. Ameen

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button