Labaran siyasa

Ba da tashin hankali na ci zabe ba; Ganduje ya bayyana sirrin samun nasarar sa

Ba da tashin hankali na ci zabe ba; Ganduje ya bayyana sirrin samun nasarar sa

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya jaddada cewar ya samu nasarar lashe zaben kujerar gwamna a karo na biyu ne saboda aiyukan da gwamnatinsa ta yi, ba ta hanyar tashin hankali ba kamar yadda wasu ke zargi.

Ganduje, wanda ya yi takara a karkashin inuwar jam’iyyar APC, ya bayyana hakan ne a fadar gwamnatin Kano yayin da ya karbi bakuncin shugabannin kananan hukumomin jihar 44 da suka kai ma sa ziyarar taya murna da jaddada goyon baya.

Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana cewar Ganduje ne ya samu nasarar a kan abokin hamayyar sa, Abba Kabir Yusuf, wanda ya yi takara a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Ba wai tashin hankali ne ya bani nasarar ba; aiki tukuru da addu’a ne sirrin samun nasara ta. Mun yi aiki tukuru kuma mun yi addu’a. Ni mai son zaman lafiya ne,” a cewar Ganduje.

Ganduje ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar APC da kada su takali ‘yan jam’iyyar adawa saboda kar a samu tashin hankali ko barkewar rigima, sannan ya kara da cewa shi da gwamnatin sa basa rigima da jam’iyyar adawa.

“Mu masu son zaman lafiya ne kuma zamu tabbatar an samu zaman lafiya koda yaushe.

 Zamu bullo da sabbin tsare-tsare da cigaba da aiyukan alheri da mu ka faro domin nuna jin dadin wannan nasara da mu ka samu

“Za mu cigaba da aikin da jama’a suka zabe mu saboda shi; shine cigaba da aiyukan gina kasa da gina rayuwar jama’a “Wannan nasara ta nuna cewar mutanen jihar Kano sun amince da mu, a saboda haka ba zamu basu kunya ba,” a kalaman Ganduje.

Kazalika ya bayyana cewar zai yi aiki da ragowar kungiyoyin hamayya da suka bashi goyon baya kafin zabe.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button