Labarai

Anyi Babban Rashi a Nigeria Bayan Tsohon Shugaban Alkalai Ya rasu

Tsohon CJN Idris Kutigi ya bar Duniya yana da shekaru kusan 80 da haihuwa 


Dazun nan labari ya shigo mana daga Jaridar Punch ta Kasar nan cewa Tsohon Shugaban Alkalan Najeriya Idris Kutigi ya cika. Babban Alkalin ya rasu ne a wani asibiti da ke Garin Landan a Ingila bayan rashin lafiya da yayi. 

Babban Yaron Alkalin Alkalan kasar watau Sani Kutigi shi ya tabbatarwa ‘Yan Jarida rasuwar Mahaifin na su. Idris Kutigi ya cika ne a kasar waje bayan yayi ‘yar budurwar rashin lafiya inda yayi jinya a wani babban asibiti a Kasar Birtaniyya. 
An haifi Idris Kutigi ne a karshen shekarar 1939 inda ya kai kololuwar aikin sa a 2007 bayan da aka nada sa Alkalin Alkalai na Najeriya. Alkali mai shari’a Kutigi ya rike wannan mukami ne har zuwa karshen 2009 lokacin da yayi ritaya. 
Kamar yadda mu ka samu labari, Mai shari’a Idris Kutigi ya rasu ya bar ‘Ya ‘ya 18 da kuma Jikoki fiye da 40. Kutigi ya rike mukamin Kwamishinan shari’a a Jihar Neja kafin a nada sa Alkalin babban Kotun Tarayya a cikin shekarar 1976. 
Anyi Babban Rashi a Nigeria  Bayan Tsohon Shugaban Alkalai Ya rasu
Babban Mai shari’ar ya soma aiki da Kotun koli ne a 1992 inda ya shafe shekaru da-dama. Daga baya kuma dai aka aika sunan babba Alkalin ya maye gurbin Salihu Alfa Belgore a matsayin Shugaban Alkalai na Najeriya gaba daya. 
Yanzu haka dai Iyalin Marigayin su na shirya yadda za a dawo da gawar mamacin Najeriya domin ayi masa Sallah. Sani Kutugi ne ya bayyanawa manema labarai hakan ba da jimawa ba. Asalin Kutigi ‘Dan Jihar Neja da ke Arewacin Kasar. 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button