Labarai

An zakulo badakala a hukumar jin dadin alhazai ta kasa (NAHCON)

A yau, Ahamis, ne kwamitin wucin gadi da majalisar dattijai ta kafa domin binciken al’amuran hukumar kula da alhazai ta kasa (NAHCON) ya mika rahotonsa mai shafi 34 ga majalisar.

Kwamitin ya gudanar da bincike ne a kan hukumar NAHCON ke kashe kudaden da take karba daga gwamnati da kuma na maniyyata, musamman a bangaren kamawa alhazai muhalli, ciyar da su, zirga-zirgar su da sauran su.

Kwamitin ya bayyana cewar badakalar NAHCON ce sanadin tsadar kudin zuwa aikin Hajji tare da bayyana yadda hukumar ke tunanin za ta iya kashe dukkan kudin da ke aljihunta ba tare da an bincike ta ba.

Kwamitin ya bayar da misalin yadda hukumar jin dadin alhazan wasu kudade da tuni ke cikin kunshin kudin da kowanne alhaji ya biya.

A cewar kwamitin, NAHC ta sanar da hukumomin jin dadin alhazai na jihohi cewar kudin aikin Hajji zai kasance N712,500.000 amma jihohin su ka kara shi zuwa N1,474,875,000 sannan su ka kara karbar dalar Amurka $1.33 daga kowanne alhaji a matsayin kudin tsaro.

Kwamitin ya kara da cewar aka yi da adadin alhazai 75,000 na shekarar 2017, an karbi kimanin dalar Amurka $5,502,750.

A cewar kwamitin wannan misali daya ne kawai daga cikin irin manyan almundahana da ta zakulo na faruwa a hukumar ta NAHCON.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button