Labaran wasanni

An Yi Allahwadai Da Matakin Da Kano Pillars Ta Dauka Kan ‘Yan Wasanta

ya ce wani lokacin dan wasa baisan abin da yayi a kungiyarsa ba zaiga an bashi takardar kora ko dakatarwa wanda kuma hakan zubarwa da ‘yan wasan kima ne a duniya.

Ya kara da cewa babu abin takaici ma illa kungiyoyin da basa biyan ‘yan wasa hakkokinsu na albashi ballan tana maganar alawus dinsu, domin kuwa kungiyoyin da suke biyan albashi a kasar nan basu da yawa.

Wannan kakkausar suka bata rasa nasaba da mummunan hukuncin da kungiyar kwallon kafa ta sunshine Stars na garin Akure da Kano Pillars suka dauka ba akan ‘yan wasansu na kungiyar a kwanakin baya.

Ita dai Sunshine ta zurawa ‘yan wasanta ido da masu horas da ita ko biyansu albashi ba a yi, sannan anki a gayamusu dalilin yimusu hakan wanda hakan kuma ya sabawa dokar kwallon kafa.

Ita kuwa kungiyar Kano Pillars tun bayan da akayimusu dukan kawo wuka a wasan karshe na gasar Aiteo Cup, masu ruwa da tsaki a kungiyar suka baiwa ‘yan wasan hutu sannan suka ce duk dan wasan da yaji ankirshi ta wayar salula to ana bukatarsa da ya dawo daukan atisaye, wanda kuwa yaji ba a kirashi ba to inna ta gai da ashsha, ma ana yanemi kungiya

kawai domin ana zato mafiya yawan ‘yan wasan Pillars din korarsu za ayi hakan ne yasa wannan kungiya ta ‘yan wasa tayi kakkausar suka hade da Allah wadai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button