KIMIYA

An Samar Da Mota Mai Tafiya A Sama Ta Farko A Duniya

An fitar da mota ta farko dake iya yin tafiya a sama mai suna Aeromobil, wadda take da fasahohin musamman 40 a gun bikin CIKE (Na baje kolin kayayyakin da ake kerawa a Kasar Sin da wadanda ake shigo da su kasar daga waje a Birnin Shanghai). Taken aikin fitar da motar shi ne “Makoma tana nan”, wannan aiki ya zama aiki na musamman a gun bikin CIIE a wannan karo.

A gun bikin, an gabatar da sabbin fasahohi, da kayayyaki fiye da 100 a duniya, wadanda suka shaida tunanin yin kirkire-kirkire na dan Adam. Hukumomin yin nazari da kamfanonin samar da kayayyaki na kasa da kasa sun fitar da sabbin fasahohi, da kayayyaki karo na farko a gun bikin CIIE, a wani mataki na kara maida hankali sosai ga kasuwar kasar Sin, da kuma kokarin da Sin ta yi wajen tabbatar da ikon mallakar ilmi a shekaru da dama da suka gabata.

A halin yanzu, kasar Sin ta shiga matsayi 20 na gaba, a jerin sunayen kasashe da suka fi yin kirkire-kirkire a duniya, wanda hukumar kula da ikon mallaka ta duniya ta gabatar. Aikin yin kirkire-kirkire ya sa kaimi ga kasar Sin, wajen samun ci gaba mai inganci. Kana kasar Sin ta shiga dukkan yarjejeniyoyin tabbatar da ikon mallakar ilmi na duniya, yayin da yawan tambarin cinikin da aka nema, da yiwa rajista ya kai matsayin koli a duniya a shekaru 16 a jere, kana yawan rokon mallakar fasahohi ya kai matsayin koli a duniya a shekaru 7 a jere.

A matsayin muhimmin dandalin tattaunawa na ikon mallakar ilmi da aka gudanar a gun bikin na CIIE, taron tabbatar da ikon mallakar ilimi, da yin kirkire-kirkire na duniya da aka gudanar a ranar 6 ga wannan wata, ya ja hankalin jami’ai, da masana, da wakilai daga kasashe da yankuna, da hukumomin duniya fiye da 20, wadanda suka tatttauna kan batun tabbatar da ikon mallakar ilmi, da samun ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire, da samar da yanayin ciniki na duniya mai inganci. Wannan ya shaida cewa, kasar Sin ta dauki alhakinta wajen tabbatar da ikon mallakar ilmi na duniya.

(Mai Fassarawa: Zainab Zhang, ma’aikaciyar sashen Hausa ta CRI)

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button