Labaran siyasa

An sako Buhari a gaba a kan satar basira a salon kamfen dinsa

Ana zargin shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC da satar basirar tambarin salon kamfen din 2019

– A dai ranar Lahadi 18 ga watan Nuwamba ne Buhari ya kaddamar da kamfen dinsa mai taken mataki na gaba wato ‘Next Level’

– Ma’abota bibiyar yanan gizo sun bincike wani shirin ilimi na Amurka mai suna ‘Next Level’ wadda tambarin shirin ya yi kama da na kamfen din Buhari

Ma’abota kafafen sada zumunta na yanan gizo sun sako Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar All progressives Congress (APC) a gaba bisa zargin su da satar basirar tambarin (Logo) yakin neman zabe daga kasan waje inda suka gabatar a matsayin na su.

Shugaba Buhari ya kaddamar da yakin neman zabensa ne a ranar Lahadi mai taken ‘Next Level’ inda ya yi bayanin cewa shekarun ukun da suka shude a cikin mulkinsa ya dora kashar kan turbar cigaba, yanzu kuma lokaci ne da za a shilla mataki na gaba na gina kasa da inganta rayuwar al’umma.

Sai dai a halin yanzu ba kalaman shugaban kasar bane ke daukan hankalin mutane amma kamanceceniyar tambarin na ‘Next Level’ wanda ke da rubutun ‘x’ mai tsawo da ke nuna alamar cewa an amince da aikin da mutum ya gabatar.

Idan aka rubuta kalmar Next Level a shafin bincike na Intanet za a iya ganin wani shiri karkashin Jami’ar Winthrop da tayi hadin gwiwa da Fort Mill School District (York 4) a yankin Lancaster da yankin Rock Hill (York 4).

Wani shiri ne na koyar da harshen turanci a karkashin sashin ilimi na Amurka wadda gwamnatin Amurkan ta dauki dauyi. A wannan tsarin Next Level na nufin hadin gwiwa domin inganta koyar da harshen turanci a mataki daban-daban.

Idan mutum ya yiwa wannan tambarin kalo guda kawai zai gane cewa akwai kamanceceniya da tambarin yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari. Masu bibiyar shafukan sada zumunta suna yada hotunan tamburan biyu inda kowa kai tofa albarkacin bakinsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button