Labaran Duniya

An kashe wata yarinya a Nigeria don yin tsafi da sassan jikinta

‘Yan sanda sun shaida wa BBC cewa an kashe wata yarinya ‘yar shekara 17 a Najeriya don a sayar da sassan jikinta wajen yin tsafin da wasu suka yi amanna yana kawo arziki.
An kama mutum uku da suka hada da wani mutum wanda ya yi ikirarin kashe ta da sayar da sassan jikinta ga wani matsafi a kan dala 25, daidai da naira 9,000.
Wani mai magana da yawun ‘yan sanda ya kuma ce bayan haka ne kuma sai mutumin ya jefa gangar jikin yarinyar a wata rijiya da ke kauyen Idosemo a jihar Ogun. A Najeriya dai wasu mutanen sun yi amanna da al’amarin tsafi sosai.
A kan je wajen bokaye ko matsafa don neman maganin wasu cututtuka, kuma masu bin su sun yarda cewa suna da siddabarun da za su iya kawo musu sa’a a rayuwa.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Abimbola Opeyemi, ya ce matsafin, wanda tuni shi ma aka kama shi, ya bayyana cewa lallai ya karbi sassan jikin mutum, amma ya ce ba shi ya bayar da umarnin kisan ba.
Ya ce an kai wa yarinyar hari ne a lokacin da take talla a kan hanya. Mahaifinta ne ya kai rahoton batanta wajen ‘yan sandan yankinsu. Mista Opeyemi ya ce, aikin hadin gwiwa da aka yi tsakanin ‘yan sanda da ‘yan sintiri ne ya sa aka kama matsafin, wanda ya amsa laifinsa a yayin da ‘yan sanda ke tuhumarsa. Ya kara da cewa hakan ce ta sa har ‘yan sanda suka gano rijiyar da aka jefa yarinyar. Har yanzu dai ba a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu ba.
Wannan kisan gilla dai shi ne na baya-baya da ya faru a kudu maso yammacin kasar, inda dama hakan na yawan faruwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button