Labaran wasanni

An Kara Yawan Kasashe A Gasar Cin Kofin Duniya Zuwa 48

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa Gianni Infantino ya ce kasashe 48 ne za su halarci gasar cin kofin duniya wacce za a yi a kasar Katar a shekara ta 2022 idan lokaci yayi.
A baya an shirya fara amfani da tsarin kasashe 48 ne a shekarar 2026, inda kasashen Amurka da Canada da kuma Medico za su karbi bakuncin gasar wadda aka basu watanni biyu da suka gabata.
kasashe 32 ne suka halarci gasar ta bana wadda aka yi a kasar Rasha kuma kasar Faransa ta lashe gasar bayan ta doke kasar Crotia daci 4-2.
Sai dai wannan sauyin zai tilasta wa kasar Katar ta hada gwiwa da wasu kasashe a yankin Gabas ta Tsakiya don karbar bakuncin gasar domin ba karamin aiki bane, a cewar shugaban hukumar
“Muna duba yiwuwar hakan, muna tattaunawa da abokanmu a Katar da sauran kawayenmu da ke yankin kuma muna fatan hakan mai yiwuwa ne domin cigaba ne babba sannan wasu zasu sake samun dama.” In ji Gianni Infantino
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana a babban taron hukumar kwallo kafa ta nahiyar Asiya a sabuwar hedkwatar hukumar a birnin Kuala Lumpur a kasar Malaysia inda yace yana so a kara bai wa kowace kasa damar fafatawa a gasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button