Labaran Duniya

An kama wani Fasto da wasu Mutane 2 akan kisan yar shekara 19 domin Asiri

An kama wani Fasto da wasu 2 akan kisan yar shekara 19 domin asiri
Yan sandan jihar Kogi sun kama wani malamin coci, Oluwasegun Aturu, da wasu mutane biyu akan zargin kashe wata karuwa mai shekaru 19, Mercy Moses domin yin asiri da ita.
Kakakin rundunar, ASP William Aya, ya tabbatar da kamun masu laifin ga manema labarai a Lokoja a ranar Juma’a.
Yace an kama Aturu wanda yayi ikirarin kasancewa malami a cocin Voice of Canaan Temple, Cherubim and Seraphim Aladura Church, Ozuri, a karamar hukumar Adavi dake jihar a ranar 19 ga watan Yuni.
An kama shi ne tare da Samuel Oluwasegun da Abdulmumini Yakubu, dukkansu daga karamar hukumar Ozuri, cewar shi.
A cewar yan sanda, Oluwasegun da Yakubu sun hadu da misalin karfe 10 na daren ranar 11 ga watan Yuni inda suka je shahararren mashaya dake yankin suka dauki marigayiyar zuwa wani waje da ba’a sani ba.
An tattaro cewa sun dauki marigayiyar daga mashayar a wata mota bayan sun gaisa da manajan wajen wanda aka ambata da suna Mohammed.
Da mohammed ya ga anyi kwana biyu Mercy bata dawo mashayar ba sai ya sanar da yan sanda.
Ya bayyana cewa bayan bincike da yan sanda suka yi shi ya kai ga kamun Otaru, Oluwasegun da Yakubu amma sun karyata sanin inda Mercy take.
Bayan an tsaurara bincike sai Oluwasegun da Yakubu suka tona asiri suka bayyana yadda Faston yayo hayarsu domin su samo masa yarinya mace.
A cewarsu Otaru yayi alkawarin basu kudi naira 700,000 idan suka samo masa yarinyar.
A cewarsa yan sanda sun yi nasarar gano inda Otaru yake sannan tuni suka kama shi tare da mukarrabansa.
Yace an mika gawar marigayiyar ga dakin ajiye gawa na babban asibitin Okene domin bincike.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button