Labarai

An gano wasu ‘Yan matan Chibok a cikin wasu kauyuka a Afrika

An ga Yara 57 daga cikin ‘Yan matan Chibok a Kasar Kamaru

Mun samu labari cewa an ga yara 57 daga cikin ‘Yan matan nan na Chibok da ‘Yan ta’addan Boko Haram su ka sace shekarun baya. An ga yaran ne yanzu a Kasar Kamaru mai makwabtaka da Kasar Najeriya.

Wata yarinya ta ga wasu ‘Yan matan Chibok a wasu Kauyuka da ke cikin Kasar Kamaru kamar yadda Iyayen wadannan yara su ka bayyanawa Jaridar Daily Trust. Tuni ma dai wasun su sun musulunta a hannun ‘Yan ta’addan.

Yakubu Nkenke wanda ita ce Shugaban iyayen matan na Chibok ta fadawa Jaridar Daily Trust wannan jiya. Nkenke tace Boko Haram sun raba yaran da su ka sace ne kashi-kashin inda yanzu aka ga wasu a Arewacin Kasar Kamaru.

Wata Budurwa da ‘Yan Boko Haram su ka taba sacewa a da ce ta gano wasu cikin yaran na Garin Chibok da aka sace a 2014 a cikin wasu Kauyuka na Garin Magaji da kuma Garin Mallam da ke daf da Garin Marwa a cikin Kamaru.

Wannan yarinya ta kuma bayyanawa Iyayen na su cewa tuni ‘Yan Boko Haram sun aure yaran kuma duk sun haihu. 7 daga cikin ‘Yan matan su na Kauyen Garin Magaji yayin da ake tsare kusan 50 a wani karamin kauye Garin Mallam.

Nkenke ta tabbatar da cewa duk abin da wannan yarinya ta fada gaskiya ne inda su ke nemi Gwamnatin Shugaba Buhari ta hada kai da Dakarun Sojojin kasar Kamaru wajen gano ragowar wadannan yara da aka yi gaba da su tun a 2014.

Source: legit.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button