Labaran Duniya

An damke wasu mutane 22 da ke da hannu cikin rikicin Kasuwar Magani

Hukumar Yan sandan Najeriya reshen Jihar Kaduna ta tabbatar da kama mutane 22 da ake zargi da hannu cikin ingiza rikicin da ya barke a garin Kasuwar Magani da ke karamar hukumar Kujama ta Jihar Kaduna
anarwan da fito ne daga bakin Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ahmad Abdulrahman a wata taron manema labarai da ya kira a garin na Kaduna. 
Rahotani da muka samu daga Tribune ya bayyana cewar rikicin da ya yi sanadiyar rasuwar mutane 55 ya barke ne a ranar Alhamis 18 ga watan Oktoba wanda hakan ya janyo gwamnatin jihar ta saka dokar hana fita na kwanaki biyu. 
Gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai ya ziyarci unguwar a ranar Juma’a inda ya yi kira ga al’ummar da su zauna lafiya da juna inda kuma ya dau alwashin binciko wadanda suka tayar da rikicin tare da hukunta su. 
El-Rufai ya zaga cikin garin tare da shugabanin addini da masu sarautun gargajiya na unguwar domin gane wa idanunsa abubuwan da suka faru a garin. 
Kamfanin dillanci labarai NAN ta ruwaito cewar wani rikicin mai kama da wannan ya taba faruwa a watan Fabrairun wannan shekarar inda a kalla mutane 10 suka rasa rayyukansu. 
Bincike ya nuna cewa a kalla mutane 65 ne aka samu da hannu cikin wancan rikicin kuma an gurfanar da su a kotu amma har yanzu ba’a kammala shari’an ba. 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button