Labaran Duniya

An Damke Mutum Tara Da Suka Yi Wa Mahaukaciya Ciki

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da damke ‘yan gudun hijira 9 da laifin yi wa wata mahaukaciya ciki a sansanin ‘yan gudun hijira na Malkohi.
‘yan gudun hijiran sun kasamce dukkan sun matasa ne kuma sun fito ne daga garin Bama ta jihar Borno suna yaudara mahaikaciyar ne zuwa wani lungu a cikin sansanin ‘yan gudun hijirar inda suke layi suna yin lalata da ita.
Jami’in watsa labarai na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Othman Abubakar, ya ce, ofishin ‘yan sanda nan Kofare suka yi bincke a kan matasan kafin a gurfanar da su a gaban kotu don ayi musu shari’a laifin da suka aikata.

Shugaban hukumar NEMA a jihar, Abbani Imam, ya ce, a lokacin da hukumar ta samu labarin aukuwar lamarin suka kafa kwamiti don bincikar yadda lamarin ya faru. Kwamitin ya haxa da jami’an sojoji da sauran jami’an tsaro, bayan da suka tabbatar da gaskiya lamarin ne suka miqa su ga ‘yan sanda don su ci gaba da binciken su da kuma gabatar das u a gaban kotu.
Duk qoqarin gano ‘yan uwan mahaukaciyar da aka yi a ciki bai samu nasara ba, bayanai sun nuna cewa, matar da aka yi wa cikin ta gamu da lalurar haukan ne sakamakon harin da ta shiga na tashin hankalin Boko Haram, a halin yanzu kuma ta na nan a sansanin ‘yan gudun hijirar ba tare da wani kulawa ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button