Labarai

An bayar da shawarar sauke sarakunan da ke da hannu a rikicin Zamfara

An bayar da shawarar sauke sarakunan da ke da hannu a rikicin Zamfara


Image copyrightGOOGLEGwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle
Image caption

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle

Kwamitin gano tushen matsalar tsaro a Zamfara ya bukaci a sauke wasu sarakuna da hakimai da dama da ya ce ya gano suna da hannu dumu-dumu a kashe-kashen jihar.
A ranar Juma’a ne Shugaban kwamitin, tsohon sufeto janar na ‘yan sanda M. D Abubakar ya gabatar da sakamakon binciken kwamitin ga gwamnan jihar, Bello Matawalle.
Wani mamba na kwamitin, Sanata Sa’idu Dansadau ya shaida wa BBC cewa gwamnatin jihar ta Bello Matawalle ta kafa kwamitin ne domin lalubo bakin zaren rikicin da ke ci gaba da ta’azzara a jihar.
Kwamitin ya kuma bayar da shawara gwamnatin tarayya ta karrama wani basarake da ya yi bajinta sannan a yi wa wasu jami’an tsaro da na shari’a daga cikin wadanda ake zargin ritaya.
A cewarshi, ”babu kage a binciken da muka gudanar wanda ya bankado ‘yan sandan da masu shari’a suna da hannu a ko dai haddasa fitinar ko kuma kara habaka ta.”
Kusan kimanin sama da mutum 3,700 ne suka bayyana gaban kwamitin sakamakon tarin takardun korafin da aka gabatar musu. ‘Yan ta’addan da suka tuba da Fulanin da aka sace shanunsu sun yi bayani dalla-dalla abin da ya ba wa kwamitin damar gano wadanda ke da hannu a wannan al’amari In ji Dansadau.
Ya ce: ”Mun yi kiyasin cewa ana bukatar naira biliyan 125 domin ilmantar da marayun da suka rasa iyayensu sanadiyyar hare-haren na jihar Zamfara sannan mun ba da shawarar gwamnatin tarayya ta taimaka wa gwamnatin jihar wajen kafa asusun neman taimako wanda zai tara naira biliyan 50 domin agaza wa mutanen da suka tafka asara sanadiyyar rikicin.”
Sanata Dansadau ya kara da cewa mutanen da aka kashe sanadiyyar rikicin sun bar zawarawa sama da dubu shida bayan marayu dubu 25.
uni gwamna Bello Matawalle ya yaba wa kwamitin bisa kokarinsa inda kuma ya ba da tabbacin ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma kamar yadda ya alkawarta zai yi.
Ya kuma ce ba zai bari son-rai ya rinjayi matakin aiwatar da rahoton kwamitin ba.
Gwamnan ya kara da cewa zai gana da Shugaba Muhammadu Buhari don jin karin wasu shawarwarin daga bangaren gwamnatin tarayya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button