Kannywood

An bawa Hadiza Gabon kyautar dankareriyar motar alfarma, hoto

Fitacciyar jaruma masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Hadiza Gabon, ta yi murnar samun kyautar motar alfarma daga wurin wata kawar ta, Laila Ali Usman, shugabar kamfanin L and N interiors.

Jarumar ce da kanta ta sanar da labarin samun kyautar motar a shafinta na sada zumunta, wato Instagram tare da mik godiya ga aminiyar ta, Laila.

Hadiza Gabon ta rubuta “ina godiya Madam kudi, sabuwar mota ta @landinteriors ina godiya,” cikin harshen turanci.

Tuni abokan sana’ar ta da na arziki ke cigaba da tururuwar turo sakon taya murna ga jaruma Hadiza Gabon.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button