Labaran siyasa

An bankado wata badakalar Naira biliyan 35 na kudin makamai

– An bankado wata badakalar Naira biliyan 35 na kudin makamai a gwamnatin tarayya

– An bankado badakalar ne a hukumar tsaron tarayyar Najeriya
– Badakalar ta faru ne daga shekarar 2007 zuwa 2015 Wani kwamitin shugaban kasa dake binciken kwa-kwaf akan kudaden da aka fidda na siyen makamai ga jami’an tsaron Najeriya daga shekarar 2007 zuwa 2015 ya gano wata badakalar Naira biliyan 35 a ma’aikatar hukumar tsaro a tarayyar Najeriya.

An bankado wata badakalar Naira biliyan 35 na kudin makamai a gwamnatin tarayya Source: Depositphotos 

Kwamitin dai a wani rahoton da ya fitar na wucin gadi a karo na hudu da kuma majiyar mu ta samu ya fallasa cewa kudin da aka bannatar bashi gwamnatin tarayya ta ciwo su a lokacin domin kara tabbatar da tsaro a kasar. NAIJ.com ta samu haka zalika cewa kwamitin ya kara gano cewa hukumar ta tsaro a lokacin bata bi dukkan hanyoyin da ya kamata ba wajen yin anfani da kudaden bashin. 

Daga karshen kuma kwamitin ya bayar da shawarar cewa gwamnatin tarayyar ya kamata ta binciki lamarin da idon basira da nufin zakulo masu laifi da kuma hukunta su. A wani labarin kuma, Mun samu labarin cewa an tashi ba’a cimma matsaya ba a wani zaman sasanci da aka so yiwa ‘yan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da wasu jiga-jigan jam’iyyar. Kamar dai yadda muka samu, taron wanda aka gudanar a ofishin uwar jam’iyyar a garin Abuja ya samu halartar shugaban jam’iyyar ta PDP Cif Uche Secondus, gwamnonin jam’iyyar ta PDP da sauran jiga-jigan jam’iyyar. 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button