Cuta da Maganin ta

AMFANIN RAKE A JIKIN DAN ADAM

AMFANIN RAKE A JIKIN DAN ADAM
=============================
A wannan yanayin ne za ka ga ana tallar Rake a duk fadin garuruwan Arewa. Mutane kan kira su saya don zaki amma amfanin Rake ya wuce nan. Ga wasu daga cikin amfanin Rake nan.

1. Yana karfafa garkuwan Jiki. Yana taimakawa wajen kare cutar sanyi, mura da cutar daji.

2. Yana kara ruwan Jiki da karfi musamman ga masu aikin karfi ko aiki cikin rana.

3. Yana taimaka ma Hanta, Zuciya, Ciki, Ido, Kwakwalwa da Al’aura.

4. Yana taimakon Koda wajen hada fitsari da kyau.

5. Yana gyara Fata saboda sinadarin glycolic acid dake cikinsa.

6. Yana wanke Hakora (amma yana da kyau ka kuskure baki bayan kasha saboda kwayoyin cuta na iya samun zakin a matsayin abinci).

7. Gara ka sha Rake da ka sayi lemun kwalba don ya fi su amfani.

8. Yana maganin yunwa kuma baya da illa ga masu cutar ciwon sukari (masu fama da Type-2 diabetes su kula kada su sha da yawa).

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button