Kiwon LafiyaMagungunan Gargajiya

Amfanin Da Ganyen Mangwaro Ke Yi Ga Lafiyar Dan’adamMangwaro wanda ake kira da suna ‘mangoe’ a turance yana daya daga cikin bishiyoyin da ake amfani da tsirransu a kasar Hausa fiye da ganyensu da kuma bawansu. Tsirrai ne na kayan marmari da ake sha dan zakin da ke gare su da kuma sinadiran bitamins da ke kumshe a cikin manguro.

 A lokuta da dama za ka ji wasu na cewa ai shan manguro yana haddasa basir, watakila suna fadan hakan ne dan ganin zakin da ke gare shi. Ba abincin da ke haifar da basir face kwayoyin cuta ne na bacteria da suke haifar da basir nau’in amoebic dysentery da kuma bacilliary dysentery. Wadannan kwayoyin cututtuka idan dai aka sha manguro gurbatacce to wata matsala harma wacce tafi ta basir za ta iya faruwa kamar ciwon ciki mai tsananin gaske da ya hada da amai da gudawa.  
Dan haka akwai bukatar a duk sanda za a sha manguro to a daina shan manguron da ya lalace ko ya rube ko mai kazamta a jiki, a dunga wankewa da kyau kamin a sha. Kuma a san adadin yawan da za a sha. Ba a bukatar a farwa manguro a yi ta sha. Wata hikima ta Ubangiji a nan ita ce, idan shan ‘ya’yan manguro na haifar da basir to shi kuma ganyensa maganin basir ya ke yi.

Ganyen mangoro yana warkar da cututtuka da dama.Ga wasu daga cikin cututtukan kamar haka:

-Maganin ciwon suga. Ganyen manguro na kumshe da sinadirin tannis da kuma anthocyanins mai taimakawa matuka dan warkar da ciwon suga. Idan dai likitoci sun ba ka tabbacin cewa kana da ciwon suga, ko ya kasance ciwon na addabar ka to ga maganin da za ka jarraba. Kasashen Turawa musamman wadanda suka ci gaba da kuma kasar India sun kasance masu amfani da ganyen manguro dan warkar da ciwon suga. Za a nemi ganye 4 zuwa 5 sai a dan sabe haka ta yanda za a ji dadin tafasa shi. Sai a sanya ruwa babban kofi a tafasa a tace, sai a ajiye har zuwa da safe, washe gari a sha kofi daya madai-daici kamin a karya. 

-Ganyen manguro na maganin hawan jini. A nan za a nemi ganyen manguro sabon toho sai a sabe a tafasa a dunga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma.

-Ganyen manguro na warkar da basir : Za a nemi ganyen mai dan yawa haka a shanya a cikin rana idan ya bushe sai a dake a dunga sanya cokali daya a cikin ruwan dumi rabin karamin kofi sai a tarfa zuma a sha.

Ganyen manguro na maganin cututtukan baki, kamar su kuraje ga harshe, ko kuraje a cikin baki masu radadi, ko zubar jini daga hakora da makamantan su. Sai a tafasa ganyen a tunga sha safe da yamma. 
Haka zalika za a rinka sanya gishiri dan kadan haka a cikin ruwan a sanda aka tafasa su sai a zan wanke baki da su a kalla sau uku ga wuni. 

-Ganyen manguro na maganin kunar wuta . Sai a nemi ganyen a shanya har sai ya bushe a kone ya koma toka sai a tunga marmasawa ga inda kunar take duk da yake akwai zafi.

 -Ganyen manguro na maganin cututtukan ciki, inda ana shan ruwan ganyen wadanda aka tafasa. 

-Ganyen manguro na huce zafin jiki da rashin hutu ko natsuwa. Sai a tafasa ganyen manguro a sha a yi wanka da shi.

– Ganyen manguro na maganin cututtukan huhu kamar tari, mura, sanyin kirji da sauransu. Indan aka tafasa  ganyen sai a tunga shan ruwan.

Ganyen manguro na inganta lafiyar mahaifa da kuma samun damar haihuwa. Indan aka lazamta shan ruwan ganyen wanda aka tafasa. 

-Ganyen manguro na maganin makakin makogwaro da ciwon wuya ko kurajen da ka iya fitowa a cikin makogwaro.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button