Labarai

AL’UMMAR JIHAR KANO SUNYI MARABA DA DAWOWAR MAI GIRMA GWAMNA GANDUJE

AL’UMMAR JIHAR KANO SUNYI MARABA DA DAWOWAR MAI GIRMA GWAMNA GANDUJE
Haƙiƙa yau mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ga taron dandazon al’umma masoya, inda su ka yi masa dafifi cikin murna da annashuwa a wannan rana da ya dawo gida Jihar Kano daga birnin tarayya Abuja. Jama’a sun nuna masa ƙauna da soyayya matuƙa.
Dandazon taron al’ummar da su ka taru a wannan rana kai ka ce Jihar Kano za ta tsage saboda ɗumbin al’ummar da su ka taru su na yi wa mai girma gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje maraba da zuwa. Tare kuma da taya shi murnar samun nasara da ya yi a kotun sauraron ƙararrakin zaɓe.
Ta duk inda ka duba tun daga filin sauƙea da tashin jiragen sama na Jihar Kano, har zuwa gefan titunan da mai girma gwamna ya bi, dandazon taron al’umma ne su ke tafi da ɗaga hannun jinjina da marhabin lale da dawowar shugaba nagari jagoran jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
“Kano ta Ganduje ce, sannu da zuwa Baba Ganduje, Kano sai uban Abba”. Ire-iren kalmomin da jama’a su ka yi ta furtawa da dawowar gwamna Ganduje.
Ba shakka al’umma sun fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu sun yi dafifi sun yi wa mai girma gwamna maraba lale da dawowa gida Jihar Kano a wannan rana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button