Kannywood

AISHA HUMAIRA TA ZAMA CIKAKKIYAR JARUMA

AISHA HUMAIRA TA ZAMA CIKAKKIYAR JARUMA.
Ga duk wanda yake mua’amala a ‘yan fim yan a da wahala ya kasa ganin ko sanin AISHATUL Humaira saboda yadda ta yi suna a cikin harkar fim tsawon lokaci , kai a cikin masana’antar ma ta yi sunan da ba kowacc ‘yar fim ta yi ba.
Domin kuwa ta dade a cikin masana’antar kuma duk wata jaruma da ta isa a fadi sunan ta za ka same ta suna kawance da ita, kai bar yara ne da ita wadanda ta isa ta aike su waje komai nisan wajen a cikin ‘yan fim din, don haka ba karamin tasiri take da shi ba a cikin ‘yan fim na kannywood, don tana da karfin fada a ji.
Sai dai duk da irin wannan matsayin da Aishal Humaira take da shi tsawon lokaci ba a taba samun ta tana yin fim ba sai dai duk wata sabga ta dan fim musamman ma idan babba ne mace ko namiji to idan ba ta zama Amara kirjin biki ba to za ka same ta a sahun gaba, don haka wasu abubuwa ma da ita ake rufe kofa ake shirya su.
Wani abu da ya zo kamar da wasa a cikin ‘yan watanin nan sai gashi Aishal Humaira ta fara yin aktin a cikin wasu finafinai da ake shiryawa , hakan ya sa mutane suke mamakin yadda ta fara yin fim a yanzu, alhalin tsawon lokaci ana yi mata tayin fim din tana cewa a kai kasuwa.
Ko a yanzu da muke hada wannan labarin tana cikin yin wani aikin fim tare da Darakta Kamal S. Alkali, sai dai duk da mun nemi jin ta bakin ta a akan dalilin ta na fara yin fim a yanzu sabuwar jarumar ta ki ba mu amsa, kawai dai abin da ta fada mana shi ne ‘ka bari sai nan gaba kadan zan yi gamana da kai, don yanzu ban fara magana da ‘yan jarida ba kan lamarin fim din da na fara ba.
Sai dai wata ta kusa da ita da ba ta so mu bayyana sunan ta ba, ta shaida mace cewar a yanzu ne Aishal Humaira ta ke ganin ya dace ta fara yin fim don ita ma ta fito da kanta a matsayin jaruma amma dai daman duniya ta san ta sai dai ba a matsayin jaruma ba.
Wata majiya ma ta shaida mana cewar kudin ta ta zuba take so ta yi fim don ta kara fito da fuskar ta a duniya, don haka da gaske take yi ba da wasa ta fito yin fim din ba.
Babu mamaki dai Aishatul Humaira tana son tallata kanta ne domin kuwa in har don kudi za ta yi fim to tana da shi don kuwa ba kowacce jarumar fim ba ce za ta fada mata shiga ta alfarma da Kuma hawa babbar mota ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button