Labari

Abin Da Gwamnati Za Ta Yi Mu Janye Yajin Aiki — ASUU

Kungiyar malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU), ta bukaci gwamnatin tarayya da ta nuna kakkarfan shaida na aniyarta a kan yarjejeniyar da suka cimma a taron su, kan bukatun su a kan yajin aikin da suke ci gaba da yi.
Shugaban kungiyar Biodun Ogunyemi, ne ya fadi hakan a cikin wata tattaunawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa a Abuja, ranar Litinin, ya ce, kungiyar za ta isar da shawarar da ta zartas a kan tayin da gwamnati ta yi masu a ranar Talata.
Farfesa Ogunyemi ya ce, sabanin abin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa, kungiyar ba ta yi fatali da tayin da gwamnatin tarayya ta yi mata ba, ba ta kuma gabatar da wasu sabbin bukatun ba.
A bayan taron ne, Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya ce gwamnati tana gab da warware matsalolin da ke tsakaninta da malaman, wadanda suke yajin aiki tun daga ranar 5 ga watan Nuwamba, 2018.

Ngige ya ce, Ma’aikatar kudi da ofishin babban akanta na kasa, sun samar da shaidun biyan Naira bilyan 15.4 na alabashin malaman da aka yanke.
Ya kuma yi nuni da cewa, akwai shaidar tabbacin Shugaban kasa ya amince da biyan bilyan 20 na kudaden ariya na tun 2009 zuwa 2012.
Ngige ya ce, ana kan yin aiki a kan kudaden, da zaran kuma an kammala za a sakewa kungiyar ta ASUU kudaden, gami da sauran bukatun kungiyar.
“Muna ta nazartan tayin na gwamnati, mun kammala tuntuban wakilanmu. Muna sa ran zuwa gobe za mu bayar da amsar mu ga Ministan kwadago da samar da aikin yi.
“Cewa muke yi ba tilas ne mu sami dukkanin bukatun namu ba, muna cewa ne in har gwamnati za ta biya mana ko da guda daya ne daga cikin bukatun namu biyar, hakan zai taimaka wa dalibai da ma kasa bakidaya.
“A maimakon mu ce, sai gwamnati ta sake mana Naira tiriliyon guda, wanda mun san ba mai yiwuwa ne ba, to akalla sai gwamnati ta sake mana kashi guda cikin biyar wanda za mu iya kasa shi a sauran sassan hudu, a fara daga zangon farko na yanzun.
A kan batun biyan malaman kudaden alawus din su kuwa ya ce, gwamnati ta yi alkawarin biyan Naira bilyan 20, sauran kuma za ta biya shi sau hudu, amma ba ta bayyana tsawon lokacin da za ta dauka tana yin hakan ba.
“Wakilanmu suna cewa ne, in har yanzun ma alkawarin biyan ake yi, to a bamu cikakkiyar shaidar da za ta tabbatar mana da hakan.
Shugaban kungiyar ya ce, wakilan na su so suke yi su tabbatar da shadar shigan kudadaden na su a cikin asusun ajiyar su, duk da sun ga tabbacin hakan a kan takarda.
“An yi mana irin wannan alkawarin na wannan bilyan 20 din a 2017, gwamnatin ta yi alkawarin biyan bilyan 20 din kashi biyu, a watannin Satumba da Oktoba, 2017, wanda kuma duk ba ta cika alkawarin ba, har sai da muka tafi yajin aiki a 2018.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button