Al'ajabi

Abin Al’ajabi baya karewa a duniya

Jami’an ‘yan sanda a Cleveland sun yi tsammanin samun wani mutum da laifin shaye shaye yayin da ya yi da kiran su a wayar sa ta hannu yana neman dauki domin a cewar sa wani alade ya yi ta bin sa tun daga tashar jirgin kasa har zuwa gidan sa.

Yayin da jami’an suka isa gidan mutumin dake zama a arewacin unguwar Ridgeville, dake Ohio, a kasar Amurka, sai suka sami mutumin cikin hankalin sa da kuma aladen da mutumin ya yi karar cewa ya hana shi sakat, duk inda ya shiga aladen nan na biye da shi.
Abin mamaki da bai taba karewa, jami’an suka kama aladen suka mayar da shi tashar jirgin da mutumin ya yi korafin fara haduwa da aladen, sai kwatsam wannan dabba ta sheka da gudu zuwa warin wani mutum da ba’a bayyana sunan sa ba, lamarin da ya ba jama’a mamaki domin aladen ya gano ainihin uban gidan sa, da ya yi tsammani wancan mutumin na farko ne.
Sabanin yadda mutane musamman a nahiyar Afirka ke kiwon kare da mage, mutane kan kiwaci maciji, alade, zomo, kadangare da sauran dabbobi makamantan su kuma su shaku da juna tamkar mage ko kare da uban gidan sa, har ma su koya masu wasu abubuwa na daban kamar yadda suke bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button