Labaran Duniya

A cikin shekara 1: An samu rahoton cikin shege 1,371,000 a Nigeria

An samu rahotonni da ke nuna cewa, a cikin shekarar 2018 kacal, an samu cikin shege 1,374,000 (sama da miliyan daya da dari ukku), kamar dai yadda hukumar tsarin kayyade haihuwar iyalai ta duniya ta wallafa wannan rahoto.

A cewar rahoton, a cikin wannan shekarar da muke ciki ta 2018, an zubar da ciki ba bisa ka’ida ba, wanda zai iya jawowa matan matsala, akalla sau 735,000 (sama da dubu dari bakwai).

Jaridar The Cable ce ta samu wannan rahoto, kuma aka bayyana ci a babban taro na kasa da kasa da ke kan gudana a Kigali, babban birnin kasar Rwanda, kan tsarin kayyade haihuwar iyali.

Rahoton ya ci gaba da bayyana cewa, sama da kashi 13.8 na matan Nigeria, na amfani da kwayoyin zubar da ciki a 2018.

Rahoton ya bayyana cikin shege a matsayin “Adadin lokacin da ake samun shigar ciki a jikin mace, a lokacin da ita macen ko shi namijinm ko kuma gaba dayansu, basu shirya zuwan cikin ba, ko karin haihuwa, ko kuma suna son bayar da tazarar haihuwa.”

“Ana auna wannan ne ta hanyar la’akari da cikin da aka dauka na baya, da kuma nazari kan cikin da aka dauka yanzu,” a cewar rahoton.

A hannu daya kuwa, masana kimiyya daga jami’ar koyon kiwon lafiyar al’umma ta Havard, ta kirkiro wani sinadari na musamman, da mata za su yi amfani da shi don daukar ciki a gaggawa.

Cikakken bayani kan hakan na zuwa…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button