Labarai
Sarkin Daura Ya Auri Budurwa ‘Yar Shekara 20 A Katsina

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar ya angwance a ranar Asabar din da ta gabata a garin Katsina.
Jaridar Katsina Post ta rawaito cewa Sarkin wanda ke da shekara kimanin tis’in (90) a duniya ya auri matar ta sa ne mai suna Aisha Iro Maikano mai shekaru ashirin a duniya kamar yadda majiyar mu ta dailynigerian.com ta ruwaito.
Auren dai an daura shi ne a cikin birin Katsina a wani taron da ba mutane da yawa a gidan Waliyyin amaryar.
Haka zalika kuma mun samu cewa an daura auren ne akan sadaki na Naira miliyan daya lakadan.