Abunda Aisha ta izzar so tayi a saudiyya baiwa magoya bayanta dadiba

Abunda Aisha ta izzar so tayi a saudiyya baiwa magoya bayanta dadiba
Fitacciyar jaruma a cikin masana’antar Kannywood mai suna Aisha Najamu wadda wasu sukafi sani da suna Hajiya Nafisa a cikin shirin nan mai dogon zango mai suna IZZAR SO.
Tuni dai mutane suka fara zarginta absa aikata wasu abubuwa a kasa mai tsarki.
Sanin kowa ne cewa jarumar tayi balaguro izuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin Umarah,sai kuma daga bisani wasu bidiyoyin ta suka bayyana a inda basuyiwa mutane da dama ba harma da masoyan jarumar dadi ba.
Cikin bidiyon an gano jarumar tare da wani mawaki kuma mazaunin kasar mai suna Majoody suna tikar rawa a shafin nan na kalli kayi shiru babu ruwanka wato TikTok.
Haka zalika wani shima shahararren a shafin na TikTok mai suna Yahaya Sheriff an gano shi tare da mazauna kasar Saudiyya din Maza da Mata ana tikar rawar TikTok.