Ba zamu lamunci Kama karyar da Kwankwaso ya keyiwa PDP a jihar kano ba- Ghali na’abba

Ba zamu lamunci Kama karyar da Kwankwaso ya keyiwa PDP a jihar kano ba- Ghali na’abba
Tsohon Dan majalisa wakilai ta kasa Ghali na’abba yace ba zasu lamunci duk wata Kama karya da shake jam iyyar PDP da wasu sukeyi a jihar kano ba matukar dai suka dawo cikin ta domin sun fuskanci yadda ake kasuwanci da Al’umma sai mutum ya Tara mutane Yana nunawa ana bashi kudi abinda Ghali yace zasu kawo gyara akanta idan har sun dawo cikin Jam iyyar PDP
Jaridar Hausafinest ta rawaito cewa Ghali na’abba ya bayyana hakane cikin wata zartarwasa da gidan radio freedom Kano Wanda yace yanzu saboda lalacewa anzo lokacin da ake rabon Mukamin Jam iyya kowa ya kawo mutanensa a saka su cikin kunshin shugabanci an daina ma maganar zabe don haka duk irin wadannan abubuwan akwai bukatar a Samar da gyara a kansu inji Ghali na’abba
Har ila yau na’abba ya bayyana takaicinsa akan yadda hatta fom din takara sai dai wani mutum ya dauka ya bawa Wanda yake so idan Kuma mutum yaje ya siya to yayi laifi da Kuma yadda yace an mayar da jam iyyar kamar wani kamfani