Labaran siyasa

2019: ’Yan Nijeriya Miliyan 83 Ne Za Su Yi Zabe –INECShugaban Hukumar zabe ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa, za a samu ‘yan Nijeriya fiye da Miliyan 83 da za su kada kuri’a bayan da aka kammala tantance kundin masu jefa kuri’a na kasar nan. 

Farfesa Yakubu ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabin maraba ga tawagar kungiyar Afrika ta yamma ECOWAS, karkashin jagorancin Janar Francis Behanzin, wadanda suka kawo masa ziyara a ofishi hukumar dake Abuja. 

Yakubu ya kuma kara da cewa, fiye da mutum Miliyan 14.5 a ka yi wa rajista a tsakanin watan Afrilu 2017 zuwa watan Agusta 2018, a karkashin shiri nan na musammna mai suna ’Continuous Boter Registration (CBR)’. 

Ya ce, za a dora sabon alkalamin nan da aka samu ne a kan mutum Miliyan 70 da suka yi ragista tun da farko wanda sunayensu kuma yaka a cikin kundin ragistar masu zabe ta kasa. 

Farfesa Yakubu ya ce, za a iya kwatanta gudanar da zabe a Nijeriya tamkar gudanar da zabe ne a daukaci yankin Afrika ta yamma ECOWAS gaba daya, ya kuma bayyana wa bakin nasa cewa, a halin yanzu akwai jami’yyu siyasa masu ragista guda 91 daga ciki kuma jam’iyyu 89 sun gabata da ‘yan takara a zabbukan da za a yi a shekarar 2019 a matakai daban daban.

Shugaban hukumar zaben, wanda ya yi tsokaci a kan kungiyar gamayyar hukumomin zabe na yankin Afika ta yamma ‘ECOWAS Network of Electoral Commissions (ECONEC)’, ya ce, Nijeriya ta cika dukkan alkawurran data daukar wa kungiyar tun bayan da ka zaben shi a matsayin shugana kungiytar a zaben da aka gudanar a gari Kotono ta kasar Benin a wata Maris na 2017. 

Ya bayyana rashin kudade a matsayin babban barazanar da kungiyar take suskanta, y ace an sanya wa kowacce kasa harajin Dala 5,000 duk shekar, ya kuma cw a kwai bukatar karunb tallafi daga kasashen kungiyar ta ECOWAS. 

Ya ce, ya samu labarin cewa, ECOWAS za ta ba kungiyar ECONEC tallafin Dala Miliyan 1, saboda haka ya yi addua’a dewa, zuwa wanna ziyarar ya zama an cuika musu alkawarin ciki a da karamin lokaci.

Tun da farko, Janar Behanzin ya mika godiyarsa ne ga shugaba hukumar INEC a bisa gudummawarsa wajen karfafa tsarin zabe a yankin Afrika ta yamma gaba daya. 

Janar Behanzin daga cikin dalilin ziyarar ta su shi ne kokarin sanin shirin da hukumar INEC suka yin a fuskantar zaben 2019 musamman ganin yawan alumar Nieriya wadanda suka isa jefa kuri’a na Miliyan 80. 

Ya ce Nijeriya babbar kasa ce, ya kuma yi alkawarin bayar da taklafin kudade wajwn gudanar da zaben. 

Ya kuma bayyana wa shugaban na INEC cewa, kungita ECOWAS za ta turo masu lura da yadda za a giudanar da zabe su 200

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button