Labaran Duniya

2019: Wani matashi ya yi barazanar kashe kan sa idan Buhari na ci zabe ba

Wani matashi a Abuja ya ja hankalin jama’a a Abuja bayan ya bayyana cewar zai kasha kan sa matukar shugaba Buhari bai ci zaben 2019 ba.

Matashin da ya yi barazanar kashe kan sa idan Buhari bai ci zaben 2019 ba Source: Facebook 

“Ina tafiya a unguwar Garki, Abuja, na ga wannan matashi dauke da fosta da rubutun cewar zai kasha kansa idan Buhari bai ci zaben 2019 ba,” kamar yadda Bagudu ta rubuta a shafinta na Facebook. 

A wani labari na da wata jarida ta buga, kun ji cewar wani saja a hukumar ‘yan sandan Najeriya ya kashe wani mutum ta hanyar caccaka masa kwalba saboda ya ki jin gargadin da ya yi masa na ya daina neman tsohuwar matar sa. 

Lamarin ya faru ne ranar Lahadi a garin Oteri dake karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta. Sai dai an kama dan sandan, Ijeoma, tare da tafiya da shi ofishin hukumar ‘yan sanda na Patani. An garzaya da David Ogbodo, mutumin da aka cakawa kwalbar, zuwa babban asibitin karamar hukumar Ughelli inda aka tabbatar da mutuwar sa saboda ya rasa jini mai yawan gaske. Wasu rahotanni sun bayyana cewar auren saja Ijeoma da matar sa, Patience, ya dade da samun matsala amma tunda ba ai saki ba ya saka shi cigaba da saka ido a kan al’amuran matar tasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button