Labaran siyasa

2019: Kwankwaso ya ba tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan hakuri

Mun samu labari cewa daya daga cikin masu takaran Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP Rabiu Musa Kwankwaso ya ba tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan hakuri a bainar jama’a a jiya. 


Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ba Dr. Goodluck Jonathan hakurin abin da ya faru a baya lokacin yana mulki. Rabiu Kwankwaso ya nemi Jonathan da Mataimakin sa watau Namadi Sambo su yafe masa sa-in-sar su a baya. 

‘Dan takarar Shugaban kasar yayi wannan jawabi ne jiya da dare lokacin da aka ba masu neman takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP minti 5 su yi takaitaccen jawabin inda su ka dosa kafin a fara zaben fitar da gwani a jiya. 

Tsohon Gwamnan Jihar Kano ya nuna cewa a lokacin da, sun dauka cewa ba a taba samun shugabancin da ya tabarbare irin sa’ar da Jonathan yake mulki ba. Kwankwaso yace sai dai yanzu an yi walkiya sun gane gaskiyar zance

Yanzu dai ana neman tsaida ‘Dan takarar Shugaban kasa a PDP Tanimu Turaki, Sule Lamido, Attahiru Bafarawa. Sauran ‘Yan takarar sun hada da Dr. Yusuf Baba-Ahmed, Ahmad Makarfi, da Ibrahim Dankwambo da sauran su. 


SOURCE: NAIJ.NG

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button