Labaran siyasa

2019: Atiku zai habbaka tattalin arziki sannan ya tura barayi kurkuku – PDP

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ce dan takarar ta, Atiku Abubakar zai habbaka tattalin arzikin Najeriya ta hanyar zamar da lafiyayyun ayyukan yi ga matasa idan har aka zabe shi a zaben shekara mai zuwa.

Jam’iyyar ta ce Atiku zai kuma sake fasalin lamuran siyasa da tattalin arzikin kasar da zai kawo hadin kai, ci gaba a gwamnati da kuma inganta rayuwar dukkanin mutanen kasar.

PDP ta jaddada cewa idan aka zabi dan takarar ta ba zai bata lokaci ba wajen fara talallata hajar Najeriya ga kasashen kasuwanci sannan kuma zai mayar da kasar yadda zata zamo abun jan hankali ga kasuwannin duniya.
Babban sakataren labarai na jam’iyyar, Mista Kola Ologbondiyan, a wata sanarwa a Abuja a ranar Lahadi, 21 ga watan Oktoba ya kara da cewa Atiku zai yi yaki da cin hanci da rashawa da zaran a zabe shi ta hanyar karfafa hukumomin doka suyi aikinsu yadda ya kamata, yayinda shi kuma zai mayar da hankali wajen shugabanci da ceto mutanen kasar daga yunwa, talauci da kuma yawaan kashe-kashe.
Ya kara da cewa shugabancin Atiku zai yi yaki da rashawa sannan ya tura barayi gidan yari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button