Bamu Karbi Ko Naira Daga Ganduje Ba Karya Ake Masa — Hukumar EFCC
Ga Abinda EFCC Tace Game da Sharrin Da’akayima Gwamna Ganduje Kan Batun Cewa Ya Bata Tallafin Naira Million Goma Wanda Kuma Kafyane….
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta yi watsi da wani rahoto da ke yawo kan cewa ta karbi tallafin naira miliyan 10 daga hannun Dr Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano. Hukumar yaki da rashawar a wani jawabi da ta saki a ranar Litinin, 26 ga watan Nuwamba ta bayyana rahoton a matsayin mai dore kai, mara tushe sannan kuma makirci. Ta ce an shirya rahoton ne da gangan a yunkurin lalata kokarinta na yakar cin hanci da rashawa.
EFCC ta kuma bayyana cewa bata karbi tallafi ba daga gwamnonin jiha, gwamnati ko kuma wani mtun ba, inda ta bayyana cewa hakan tsarinta ne. Ta yi bayanin cewa ana daukar nauyin hukumar ne ta kasafin kudi da wasu kasa-kasai ta kuma bayyana cewa babu wani gwamnan jihar ko wani ko kungiya da ta bata tallafin ko sisin kwabo don ta gudanar da aikinta na yakar cin hanci da rashawa. -ba