Labarai
Kalli hotunan yan shi’a a lokacin da suka shiga fadar shugaban kasa
Rahotanni sun kawo cewa kungiyar Musulman Shi’a sun yi tattaki zuwa fadar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Laraba, 4 a watan Oktoba.
A cikin hotunan an gano mabiya kungiyar maza da mata, manya dayara sanye da bakaken kaya. Hakan baya rasa nasaba da kira da kungiyar ke yi na cewa asaki shugabansu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky wanda ke a hannun jami’an tsaro tsawon wasu shekaru. Ga hotunan tattakin nasu a kasa: