Labaran Duniya
Kano ta samu sabon ‘Dan masanin Kano
Alhaji Abdulkadir Maitama Sule ya gagi sarautar ne daga mahaifin shi wanda ya rasu cikin watan Yuli na shekarar 2017.
Maganar da hausawa keyi na cewa ‘kyawun ‘da ya gaji ubansa’ ta tabbata inda mai alfarma sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi na biyu ya nada da’dan Marigayi Yusuf Maitama Sule da sarautar ‘Dan masanin Kano’.
Masarautar Kano ta nada Alhaji Abdulkadir Maitama Sule da sarautar a karshen makon da ya shude.
Ya gaji sarautar ne daga mahaifin shi wanda ya rasu cikin watan Yuli na shekarar 2017.