Rayuwa A Kauyen da Ya Fi Kowane Wuri Sanyi A Duniya
A kauyen da ya fi ko ina sanyi a duniya, girar mutum tana daskarewa ta zamo kankara, abinci na zamowa kankara, yayin da numfashi ke daskarewa da zarar ya fita daga hancin mutum.
A kauyen Oymyakon mai mutane 500 a yankin Yakutia na kasar Rasha, mutane ba su iya kashe motarsu ko da ba su amfani da ita a saboda baturinta na iya mutuwa kwata-kwata saboda tsananin sanyi idan suka kashe motar.
Girar mutum ta kan daskare ta yi kankara daga numfashin da ya fito hancin mutum, ko kankara ta taru a gashin baki, duk da cewa kusan ya zamo dole mutum ya rufe ko ina a jikinsa, har fuska, musamman idan ana iska a lokacin sanyi.
A ranar lahadi da ta shige. na’urar auna sanyi (thermometer) da kauyen ya saya ya kafa a cikin gari don duk mai wucewa ya iya ganin irin matsayin sanyin da ake yi, ta lalace ta fashe, a lokacin da awun sanyi ya kai mizani 88 a kasa da mizanin daskarewar ruwa.
A lokacin hunturu a wannan kauye, kwata-kwata awa 3 kacal rana take yi a sama, watau daga fitowarta har zuwa faduwarta. Ana zama cikin duhun dare na tsawon awa 21.
Irin wannan tsananin sanyi yana shafar kowace irin rayuwa ta mutanen wannan yanki. Alal ga misali, a lokacin hunturu kamar a yanzu, akasarin abincinsu nama ne, wanda a wani lokacin a daskarensa suke ci haka, saboda ba a iya shuka komai a kasar wurin wadda take daskarewa ta zamo kamar kankara.
Wasu daga cikin irin wadannan abinci sun hada da wanda suke kira Stroganina, watau kifin da aka fere namansa kamar kilishi, amma danye wanda ya daskare ya zama kankara. Haka kuma su na cin naman wata dabba dangin barewa da aka fi samu a dazuzzukan wurin; da kuma hantar doki da ta daskare ta zamo kamar kankara.