Labaran Duniya

Dalibai 242 Suka tafi Indiya Domin Degree na Biyu (Masters) Wanda Kwankwasiyya Foundation ta day Nauyinsu 

A yau Talata ne daliban da gidauniyar Kwankwasiyya ta tantance za su tashi zuwa jami’oi a kasar Indiya da soma karatu. 

Tun da farko, tsohon Gwamnan na Kano, Dakta Kwankwaso sai da ya mika godiyarsa ga jama’ar Kano bisa goyon baya da gudummuwa da suke bashi a bangarori daban-daban kan harkokin siyasa.
Ya ce, a rayuwa in Allah ya baka dama kayi amfani da ita wajen cigaban al’umma duba da yanda abubuwa ke tafiya ta damuwa ta bangaren tsaro, tattalin arziki, siyasa abune daya kamata mutane suyi hobbasa don kauda matsala sai a sami yanayi mai kyau a gaba.
Sanata Kwankwaso ya kara da cewa, shi ya sa suka yi hobbasa a Kano a bangaren ilimi da take da bangarori da yawa sai dai kowa ya dauki bangaren da zai iya taimako akai ya yi.
Tun daga matakin furamare in kaje zaka taras da bukatu ba iyaka haka sakandire da manyan makarantu, wasu a jihar Kano an kashe su wasu ba’a budesu ba.
Ya ce, shi ne su daga bangarensu na Gidauniyar Kwankwasiyya suka ga ya dacewar su fito da wani abu da za su dora akan abinda suka yi a baya. Kwankwasiyya ta yi aikace-aikace da dama na tallafawa da jari, auren zawarawa, biyawa dalibai makarantu a ciki da wajen kasar nan da sauran abubuwa da dama.
Kwankwaso ya ce, wannan karon sun yi tunanin kai dalibai karatu waje, mun tafi Indiya sau biyu mun duba jami’oi da abinda suke don tura yara da za su yi karatu su dawo da kyakkyawan sakamako” cewar Sanata Kwankwaso.
Ya yi bayanin cewa yara sama da dalibai 400 da suka nemi shiga tsarin an tace sun koma 370 ma’aikatar ilimi ta kasa an kai musu sun tace suma wasu basu tsallake ba. Sun tafi ma’aikatar kasashen waje nan ma wasu basu tsalllake ba, haka ma a wajen samun biza wasu basu cika ka’idoji ba.
Sun tura dukkan ka’idoji kasar Indiya na yanda za’a sami shiga makaranta an kai matsayin da duk abinda ake nema ya samu sai tafiyar wadannan yara 242 da suka yi nasarar cika ka’ida. Sanata Kwankwaso ya ce, anyi taro na neman gudummuwa mutane sun bayar sosai domin ayi wannan aiki,suna godiya ga Allah daya basu damar tsara wannan abu cikin lokaci kankani kuma suka sami al’umma masoya da suka bada gudummuwa, kuma asusun kwankwasiyya yana nan a bude ga  duk mai bada gudummuwa dan cigaba na alkhairi.
Ya ce, da akwai wadanda basu yarda za’a yi ba yanzu mafi yawansu sun yarda, sai ma sunga daliban a filin jirgin sama sun tashi za su yarda da gaske ne. Sanata Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso a wannan tsarin ba wani dan PDP ko APC ko wanda baida jam’iyya ko wannan mai son Kwankwaso ne duk babu wannan, magana ce taka cika ka’ida da aka gindiya haka aka bi har zuwa wannan matsayi.
Dukkan daliban in banda guda takwas duka Indiya  za su jami’oi guda hudu. Ragowar takwas din wanda za su karanta harkar addini da larabci ana nema musu jami’oi a tsakanin Sudan da Masar da suma za su tafi daga baya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button