Labari da dumi-dumi

GAMAYYAR KUNGIYAR SAMARI MABIYA DARIKAR SUFAYE TA KASA  TAYI ALLAH WADAI DA ABIN AKAI WA SHEIKH PANTAMI

Daga: Muslihu Yusuf Ali (National Secretary)

Wannan kungiya ta yi Allah wadai da mummunan harin da wata kungiyar adawa ta siyasa ta kaiwa babban malamin addinin musulunci kuma jagora wato sheikh isa Ali pantami,ministan sadarwa da fasaha na kasa a ranar talata 23/9/19 a filin tashin jirage na malam aminu kano da ke   jihar kano a kan hanyarsa ta komawa abuja bayan ya gabar da ta’aziyyarsa ga Hon Sha’aban Ibrahim sharada shaaban kwamitin majalisar tarayya kan sha’anin tsaro bisa rashin mahaifinsa da ya yi a sharada cikin birnin kano.

Sannan kuma muna kira da babbar murya ga su jagororin wannan kungiya da su gaggauta ba da hakuri a kan abinda ya faru.

Kuma mu na so mu yi amfani da wannan dama wajen mu yi kira ga duk alummar  musulmi na kowanne bangareko aqida da su fito su yi tofin alastine kuma su yi Allah wadai ga wannan danyan aiki da su ka aiwatar.

Signed by
USTAZ SHAM’UN MUSA GABARI.
National chairman.
_____________________
MUSLIHU YUSUF ALI
national Secretary

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button