ABIN MAMAKI

WATA MATA TA BIYAWA MIJINTA SADAKI DOMIN YAYI MATA KISHIYA

Wata mata mai suna Hajiya Saratu Arbi Kamba ta goyi bayan mijinta Alhaji Arbi da ya kara aure.

A zantawar ta da wakilinmu a yau Juma’a, Saratu ta ce “nasan mijina kuma abukiyar zama ai ba abun gudu ba ce’.

An tambaye ta lokacin da ta ji mijinta zai kara aure ya ta ji?
Sai ta ce “mijina ya zo ya same ni ya ce Saratu ina neman mata zan kara aure a garin Kangiwa, sai ta ce to Allah ya tabbatar da alheri.
An sake tambayar ta shin ba ta jin tsoron Amarya ta zo ta kwace mata miji ?

Sai tace” ni na riga na san kaunar da mijina yake mun don haka bana tunani haka zai faru.

A yayin da aka tambaye ta ko akwai wadanda suka zuga ta da kada ta yarda mijin ta ya kara aure?

Sai tace, “ehh! mata ‘yan uwana sun yi ta ingiza ni da kada in yarda amma na yi biris da maganarsu.

Ko kwai  gudumuwa da zaki iya baiwa mijinki a wannan aure da zai kara?

Ai na ba shi gudunmuwa tunda na amince ya kara aure, kuma ina da niyar biya masa Sadaki idan an yanka.

Game da ko waane sako za ta tura zuwa ga ‘yan uwanta mata wadanda ba su son kishiya, ganin ko a kwanan nan wata ta kashe mijinta!

Sai ta ce “Bana fatan in kashe mijina kuma ina kira ga mata ‘yan uwana da su sani mata hudu aka ce namiji ya yi idan yana da hali kuma ya kamata mata su sani kishiya ai abokiyar zama ce.

Daga karshe Hajiya Saratu ta yi kira ga maza da su kara aure matukar suna da hali amma su yi adalci, inji saratu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button