Labari da dumi-dumi

LABARI DA DUMI DUMI
KOTU TAYI WATSI DA KARAR DA PDP TA SHIGAR GABANTA NA KALUBALANTAR APC

Kotun sauraren karar zaben gwamna wacce ke zaman ta a miller road tayi watsi da karar da PDP watau Abba Kabir Yusuf Wanda yake kalubalantar APC Dr. Abdullahi UMAR Ganduje a nasarar da yayi a. Zaben 2019

 Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya yi gagarumar nasara a kotun karar zabe da kungiyar Kwankwasiyya ta shigar akan maganar nasarar da Gwamna Ganduje ya samu a zaben 2019. Kotun tayi pacali da karar gaba dayan ta, inda ta ce shigar yan kungiyar zagaye na biyun zaben wato rerun da akayi ya sa sun barar da damar su ta yin korafi akan halarcin rerun din. Sannan duk hujjojin da suka bayar cike suke da jita jita ba ainihin hujja ba. Sannan kuma shaidun da suka gabatar basu inganta ta ba.

Ina amfani da wannan dama na taya Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR Gugar karfe na Goggo da Mataimakin Sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna damuna baki mugunta, murnar wannan nasara da suka yi a kotu. Sannan ina jan hankali da yan kungiyar Kwankwasiyya da su yadda da Kaddara su kuma daina ja da Ikon Allah, Allah Ya ara wa Ganduje dama kuma ba wanda ya isa ya karbe ta sai waadin sa ya cika. Dan haka su hakura su bi Allah su bi Ganduje.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button