Labarai

ƘUNGIYAR GWAMNONIN APC SUN TABBATAR DA GWAMNA GANDUJE A MATSAYIN GWAMNAN DA YA FI KOWANE GWAMNA AIKI A CIKINSU

ƘUNGIYAR GWAMNONIN APC SUN TABBATAR DA GWAMNA GANDUJE A MATSAYIN GWAMNAN DA YA FI KOWANE GWAMNA AIKI A CIKINSU
A wani rahoton bincike da su ka fitar dangane da cigaban da su ka samu a fannoni daban-daban, ƙungiyar gwamnonin Nageriya ƙarƙashin tutar jam’iyyar (APC), sun tabbatar da mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gwamna mafi ƙoƙari da himma kan samar da ayyukan cigaban al’umma.
Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda da aka aikewa mai girma gwamna a ranar 7 ga watan Octoba, 2019, mai ɗauke da sa hannun babban daraktan ƙungiyar, Mallam Salihu Mohammad Lukman. Mai taken “cigaban da aka ƙirƙiro a fannoni daban-daban a jihohin da jam’iyyar (APC) ta ke mulki”.
Kamar yadda aka bayyana a cikin takardar, rahoton binciken ya tabbatar da tagomashin da aka samu a fannoni da dama na cigaba, “wanda ƙungiyar ta tattara daga Jihohin a wannan shekara ta shekarar (2019). Kuma dukkan bayanan da ta tattara su na kan manhajin tattara bayanai na al’umma, wasu bayanan kuma su na sakatariyar ƙungiyar da ke Abuja.
Da su ke yabawa kan hakan, ta kowacce fuska an samu cigaba sosai kan dabarun da aka yi amfani da su wajen ƙirƙiro abubuwan da aka gabatar a jihohin jam’iyyar (APC), takarda ta kuma kasafta cewa, “a bayannan da aka tattara Jihar Kano ita ce ta farko a wannan wata bisa cigaban da ta samar sassa (18)”.
Sassan cigaban kamar yadda takardar ta yi bayani sun haɗa da :samar da ayyukan yi, da kula da kiwon lafiya da sashen ilimi, da fannin tsaro, da fannin sufuri da fannin walwalar al’umma da na wutar lantarki da fannin noma da na shari’a da kuma fannin tsaftar muhalli.
Jihar Yobe ita ce ta biyo Jihar Kano da sassa (14), sai kuma Jihar Borno mai (13) sai kuma Edo, sai Gombe, sai Kaduna, sai Lagos, sai kuma Ogun da sassa (12) kowaccensu.
Bayansu sai kuma Jihar Ekiti wacce ta samu (11), da Nassarawa mai guda (9), da kuma Jihohin Katsina da Kebbi waɗanda su ke da guda bakwai-bakwai. Sai kuma Jihohin Kwara da Osun masu shida-shida. Daga nan kuma sai Niger mai guda (5), da Ondo wacce ta ke da (4) sai kuma Kogi da Plateau masu sassan cigaba guda uku-uku.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button